Uncategorized

Mata sun yi zanga-zanga a tuɓe kan rashin tsaro

Mata sun gudanar da zanga-zanga a tuɓe domin bayyana fushinsu kan matsalar rashin tsaro a yankin Akoko da ke Jihar Ondo.

Matan sun gudanar da zanga-zangar ne suna masu nuna damuwa bisa yawan kashe-kashe da garkuwa da mutane da kuma lalata gonaki a yankin.

Masu zanga-zangar wadanda yawancinsu tsofaffi ne suna zargin makiyaya da hannu a kashe-kashe da kuma lalata gonaki.

Sun yi tattakin nasu a tuɓe ne bayan kashe wani manomi mai suna Sunday Ayeni a yayin wani rikicin tsakaninsa da wasu makiyaya a gonarsa.

A karshen mako ne aka tsinci gawarsa bayan an yi ta neman shi, lamarin da ya sa manoma watsi da gonakinsu saboda tsoron abin da ke iya biyo baya.

A yayin taron tsaro da aka gudanar a fadarsa, Olubaka na Oka, Adebori Adeleye, ya ce masu zanga-zangar sun bukaci a bi wa wadanda aka kashe haƙƙinsu.

Mai magana da yawun matan, Misis Abigail Ojo, ta zargi makiyaya da yin fyade ga wasu mata a gonakinsu da kuma lalata musu amfanin gona.

Ta ce abin da ya faru ya sa sun yi watsi da gonakinsu, kuma ba za su koma ba sai sun samu tabbacin tsaro.

Don haka ta roki jami’an tsaro su magance matsalar baki daya.

A nasa jawabin, basaraken, Mista Adeleye, ya ce jami’an tsaro na daukar matakan magance matsalar tsaron yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button